Faransa na tattaunawa da Saudiyya dangane da batun samarda cikakkiyar kasar Falasdinu.

Faransa da Saudiyya na jagorantar wani taron tattaunawa na kwanaki uku na MDD da nufin farfaɗo da fatan samar da ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
Ga Faransa dai, wani yunƙuri ne na gina goyon bayan shugaba Emmanuel Macron na amincewa da ƙasar Falasɗinawa nan gaba a wannan shekarar.
Gwamnatin Trump dai na adawa da matakin – kuma Amurka za ta ƙaurace wa taron na MDD.
Macron na fatan matakinsa zai tursasa wa Isra’ila da ƙasashe irinsu Birtaniya su aminta, domin samar da zaman lafiyan aka kasa samu
