Fafaroma ya nuna damuwa da kama shugaban Venezuela

Fafaroma Leo ya ce dole ne a tabbatar da martabar Venezuela tare da walwalar ƴan ƙasar fiye da komai.
Jagoran ɗariƙar Katolikan na duniya – wanda ya yi aiki na kusan shekara 20 a kudancin Amurka – ya ce yana biye da abubuwan da ke faruwa a Venezuela.
Tun da farko China ta yi kiran a gaggauta sakin Shugaba Maduro, tana mai cewa Amurka ta keta dokokin duniya.
Ana sa ran Mista Maduro zai gurfana a gaban kotu ranar Litinin domin fuskantar tuhume-tuhume kan safarar miyagun ƙwayoyi da makamai, zarge-zargen da a baya ya sha musantawa.
A gobe ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taro domin tattaunawa kan harin da Amurka ta kai wa Venezuela tare da kama shugaban ƙasar da mai ɗakinsa.
