El-Rufai na son kotu ta dakatar da DSS daga tuhumarsa

0
20260217_163647
Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci babban kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar tsaro ta DSS daga ci gaba da tuhumarsa, yana mai cewa zarge-zargen da ake masa ba su da inganci kuma sun saɓa wa doka da tsarin shari’a.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata ƙara da ya shiga a gaban kotu ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar.

Ƙarar ta ce El-Rufai ya nemi a soke tuhumar da DSS ke yi masa gaba ɗaya bisa hujjar cewa ba ta bayyana wani laifi da ya aikata da doka ta tanada ba kuma ba ta nuna hujjar farko ba, kuma cin zarafin tsarin kotu ne.

Ya kuma buƙaci kotu ta wanke shi gaba ɗaya daga zargin da ake masa.Bugu da ƙari, El-Rufai ya kuma nemi kotu ta umarci DSS ta biya shi diyyar Naira biliyan biyu, yana zargin hukumar da amfani da tsarin shari’a wajen tsangwama da muzanta shi a bainar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *