Duka shugabannin ƙananan hukumomin Bayelsa sun fice daga PDP

Duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar Bayelsa takwas sun sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP, tare da nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar Douye Diri da shi ma ya fice daga jam’iyyar.
Shugabannin ƙananan hukumomin sun bayyana matakin ne da maraicen ranar Laraba a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da suka gabata a Yenagoa babban birnin jihar.
A ranar Laraba da rana ne gwamnan jihar ya sanar da ficewa daga jam’iyyarsa ta PDP, tare da duka ƴan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar.
Kawo yanzu dai gwamnan bai bayyana jam’iyyar da ya koma ba.
