Dole ne mu gyara abubuwan da ba sa aiki a Najeriya – Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce dole ne a gyara abubuwan da ba sa aiki a ƙasar tare da haɗin gwiwar ƴan kasa domin tabbatar da ci gaban al’umma da tsaron rayuka.
Tinubu ya fadi hakan ne a walimar buɗe baki da ya shirya wa gwamnoni da sauran muƙarabban gwamnati a fadar shugaban ƙasa.
Tinubu ya ce “Dole ne mu kasance masu ƙarfin hali wajen gyara abin da ba ya aiki kuma mu haɗa kai wajen kare darajarmu, ƙasar sai ta fi zama mafi aminci kuma mafi ƙarfi idan aka haɗa hannu wajen cimma waɗannan manufofi.
“A jawabin sa, Tinubu ya bayyana shirinsu na kafa ƴansandan jihohi domin magance matsalolin tsaro yana mai cewa “tsaro shi ne ginshiƙin arziki, domin idan babu tsaro, noma ba zai bunƙasa, kasuwanci ba zai girma, kuma iyalai ba za su sami natsuwa ba.
“Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnonin da su ƙara ƙarfi wajen ayyukan jin kai a wannan watan mai tsarki inda ya ce “akwai buƙatar tallafa wa matasa da mata da ke ɗaukar nauyin iyalansu, da kuma zuwa ga al’ummomin ƙananan hukumomi inda fata kan samu rauni.
“Tinubu ya kuma jaddada cewa alkawarin da ya yi wa ‘yan Najeriya ba zai samu jinkiri ba.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki tukuru wajen samar da fata da dama, da tsaro ga kowa da kow
