Dino Melaye ya zargi APC kan rikicin ADC da INEC

0
Dino Melaye ya zargi APC kan rikicin ADC da INEC

Sanata Dino Melaye

Spread the love

Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aikata abin da ya kira “shaiɗanci da mugunta” bayan matakin da Hukumar Zabe (INEC) ta dauka kan shugabancin jam’iyyar (ADC).

Melaye ya ce matakin na INEC na dakatar da amincewa da wasu shugabannin ADC yana da nasaba da siyasa, yana mai zargin APC da kokarin raunana jam’iyyun adawa domin kafa tsarin jam’iyya daya a kasa.

Ya kuma gargadi cewa irin wannan mataki na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya, tare da kira ga hukumomi da su yi adalci da bin doka wajen tafiyar da harkokin siyasa a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *