Cututtuka da dama ne ke kashe ƙananan yara ba yunwa ba – Gwamnatin Katsina

0
1000065323
Spread the love

Gwamnatin jihar Katsina a Najeriya ta yi martani kan sanarwar da ƙungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers, MSF, ta fitar wanda ke cewa aƙalla kananan yara 652 suka mutu cikin watanni 6 a jihar, sakamakon matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.

A ƙarshen makon da ya gabata ne dai kungiyar MSF ta sanar da cewa zabtare kuɗaɗen tallafi da take samu daga ƙasashen duniya na janyo tsaiko a ƙoƙarin da take yi na tallafawa harkar kula da lafiya musamman a ƙasashe masu tasowa.

Barista Bulama Bukarti ya yi sharhi kan matsalar, inda ya ce “MSF ta ce a wata shida farko kawai na wannan shekarar an kawo yara aƙalla dubu 70 a asibitocinta, a ciki kuma kimanin dubu 10 sai da aka kwantar da su sannan daga cikinsu kuma yara 650 suka mutu a jihar Katsina.”

Da take martani kan batun, gwamnatin Katsina da bakin shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko, Dr Shamsuddeen Yahaya, ya ce duk da cewa akwai cutar yunwar, akwai wasu matsalolin da suke ta’azzara matsalar.

“Mun san akwai matsalar tamowa a Katsina, kamar yadda take a sauran jihohin arewa maso yamma, hakan ya sa gwamnatin Katsina ta ware ƙarin naira miliyan 500 ɗoriya a kan naira miliyan 500 da aka fara warewa domin fuskantar matsalar.”

Sai dai ya ce duk da sun san akwai yunwa, “amma akwai wasu cututtuka da ma rashin sani da suke ta’azzara matsalar saboda misali bincike ya nuna shayar da yaro nonon uwa zalla a wata shidan farko na kare yaro daga cututtuka. Sannan matsalar tsaro na taka rawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *