Cin amana shi ne tsarin siyasa a Najeriya – Jonathan

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce siyasar Najeriya ta ginu ne a kan cin amana, la’akari da irin cin amanar da ya ce ya fuskanta matuƙa a lokacin da yake neman tazarce a Zaben 2015.
Jonathan ya bayyana haka ne a wurin bikin cika shekara 70 na tsohon abokinsa, Cif Mike Aiyegbeni Oghiadomhe, da aka gudanar a Benin, babban birnin Jihar Edo, a ranar Alhamis.
Ya ce daga cikin abubuwan da ya fahimta a siyasar Najeriya shi ne wahalar samun ɗan siyasa mai gaskiya da tsayawa a kan kalamansa.
A cewarsa, galibin ’yan siyasar Nijeriya ba su da riƙon gaskiya ko amana, sai dai ya yaba da Oghiadomhe a matsayin mutumin da ya fita daban cikin ’yan siyasar ƙasar.
