Chadi ta rufe iyakarta da Najeriya saboda barazanar Amurka

0
1000267013
Spread the love

Gwamnatin Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Najeriya nan take saboda fargabar tsaro da ta yi yawa sakamakon jita-jitar da ake yadawa game da yunkurin sojojin Amurka a wasu sassan Yammacin Afirka.

Majiyoyin soji a N’Djamena sun tabbatar a ranar Litinin cewa Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya ba da umarnin a rufe iyakar Najeriya bayan bayanan sirri sun nuna cewa ‘yan ta’adda daga Arewacin Najeriya na shirin tsallakawa zuwa Chadi.

A cewar Zagazola Makama, an tura sojojin Chadi da motocin sulke zuwa muhimman hanyoyi daga Najeriya, kuma dukkan rundunonin sun shirya tsaf.

An ruwaito cewa Shugaba Déby ya yi gargadin cewa “ba za a bar wata kungiya mai dauke da makamai ko wata rundunar kasashen waje ta shiga kasar Chadi da wani abu makamancin haka ba.

“Rufe kan iyakar ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin da kuma jita-jitar da ake yadawa game da ayyukan soji da Amurka ke yi a yankin Sahel da Yammacin Afirka.

Masana tsaro sun ce matakin na Chadi wani mataki ne na kariya da nufin kare iyakokinta da kuma hana shigar ‘yan bindiga wadanda za su iya amfani da rashin zaman lafiya a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *