Burkina Faso ta janye biyan ƙudin bizan shiga ƙasar ga ƴan Afirka

Gwamnatin sojin Burkina Faso, ta sanar da bada biza kyauta ga ɗaukacin ƴan ƙasashen Afirka da ke shirin zuwa ƙasar, sai dai masu neman zuwa ƙasar za su cika wasu sharuɗa a shafin intanet na ma’aikatar da ke da alhaki kafin amincewa zuwa ƙasar ko akasi, amma dai babu biyan ƙudin bisa kamar yadda lamarin ya ke a baya.
Gwamnatin sojin Burkina Faso ƙarƙashin jagorancin kaftin Ibrahim Traore ta yanke wannan shawarar ce bayan taron majalisar ministocin da ya gabata.
Sharadi ɗaya tilo ga ƴan Afirka da ke son ziyartar ƙasar da ke yankin Sahel shi ne cike fom ta yanar gizo kuma a amince da takardar izinin shiga kasar.
Ministan tsaron ƙasar Mahamadou Sana, wannan ya sanar da hakan ya ce, da wannan matakin, Burkina Faso na da niyyar tabbatar da burinta na ƙarfafa ɗankon zumuncin da ke tsakanin al’ummar Afirka.
Ƙudin bisa da ake biya a baya
Kafin wannan mataki na bada bisa kyauta, ƙasar na bada izinin shiga ƙasar na ɗan gajeren zama, masamman yawon buɗe ido kan ƙudi CFA 55,000 (Yuro 84), idan na kasuwanci ne kuma CFA 93,500 (€ 142).
Masu sharhi na ganin da wannan mataki, hukumomi a Ouagadougou na neman ƙarfafa ƴancin zirga-zirgar jama’ar Afirka tare da tabbatar da matsayar ƙasar na maraba da baƙi.
