Borno: Zulum ya bayar da kyautar abinci ga zawarawa Kiristoci, marasa galihu

0
1000391013
Spread the love

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba kayan abinci masu mahimmanci ga zawarawa da marasa galihu na al’ummar Kirista a shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti mai zuwa.

Mutane sama da 6,000 za su amfana da wannan tallafin, ciki har da ‘yan gudun hijira 1,605 waɗanda kowannensu ya sami buhun shinkafa, kwalin taliya 1, da galan 1 na man girki.

Taron na wannan shekarar, wanda ya gudana ranar Litinin, ya nuna ci gaba da manufar tallafawa tun lokacin da aka rantsar da shi a shekarar 2019, tsawon shekaru biyar da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *