Bauchi: Gwamna Bala ya kori kwamishinan harkokin mata

0
1000190145
Spread the love

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya kori kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara, Hajiya Zainab Baban Takko.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ta ce gwamnan ya amince da wani karamin sauyi a majalisar zartarwa ta jihar.

Gidado ya bayyana cewa, dangane da haka ne aka sauke kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara, Hajiya Zainab Baban Takko daga mukamin nata ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *