Barazanar Trump: China ta gargadi Amurka game da tsoma baki a harkokin Najeriya

0
Spread the love

Gwamnatin China ta yi alƙawarin goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar ɗaukar matakin soja.

Da take jawabi a wani taron manema labarai a ranar Talata, Mao Ning, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, ta ce China tana adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini da haƙƙin ɗan adam a matsayin uzuri don tsoma baki a harkokin cikin gida na wasu ƙasashe, tare da yi wa wasu ƙasashe barazana da takunkumi da ƙarfi.

Ning na amsa tambaya kan barazanar Trump na ɗaukar matakin soja a Najeriya saboda zargin cin zarafin Kiristoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *