Bankuna za su fara cire naira 50 a duk 10,000 da aka tura

Bankuna a Najeriya za su fara cire naira 50 a matsayin harajin da banki ke cirewa kan kudin da aka tura ko aka cire da ya wuce naira 10, 000 daga ranar 1 ga Janairun 2026 bisa sabuwa dokar haraji da aka kafa.
An sanar da hakan ne a cikin wasiƙu da bankuna suka aika wa kwastomominsu kafin fara aiwatar da wannan sabon tsarin.
Harajin yana nufin cire naira 50 kai tsaye a kan kowanne kuɗi da ya shiga ko ya fita daga cikin asusun banki da ya wuce naira 10,000.
Wannan tsarin ba zai shafin kuɗin albashin mutum da ke shiga asusun bankinsa ba da kuma kuɗin da aka tura daga banki iri ɗaya.
A da, wanda aka tura wa kudi kadai ake cirewa wannan harajin, amma yanzu tsarin zai shafi wanda ya tura kuɗin ma.
Bankunan sun fayyace cewa wannan charjin ba iri ɗaya bane da charjin da bankuna ke yi da aka saba gani ba kuma za a nuna wa mutum a lokacin da yake tura kuɗi.
