Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah

0
1000092553
Spread the love

Akalla Fulani makiyaya 20,000 aka kashe a rikicin manoma da makiyaya, yayin da aka sace musu shannu sama da miliyan 4 a cikin shekaru 5 da suka gabata, inji shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Najeriya.

Shugaban ƙungiyar Baba Usman Ngelzerma ya bayyana haka, lokacin da yake kare kan su daga zargin cewar basa ɗaga muryarsu a duk lokacin da aka samu ɓatagari daga cikin su dake gudanar da ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Ngelzerma ya ce su kan su Fulani makiyayan ba su tsira daga ayyukan waɗannan ɓatagari ba, domin ko a watannin da suka gabata, an hallaka shugabannin su na jihohin Katsina da Kwara da kuma Filato, saboda haɗa kan da suke yi da hukumomi domin dakile ayyukan ta’addanci a jihohin da suke shugabanci.

Shugaban ƙungiyar ya ce tabbas wannan matsala ta ayyukan ta’addanci ta ɓatawa Fulani suna a Najeriya, amma kuma ba dukkan su ke cikin wannan aiki ba, domin akwai Fulani na gari dake gudanar da ayyukan su cikin kwanciyar hankali, ba tare da goyan bayan ta’addancin ba.

Ngelzerma ya ce yanzu haka tsakanin Fulani makiyaya dubu 15,000 zuwa 20,000 suka fice daga Najeriya zuwa wasu ƙasashe domin tsira da rayukan su da kuma dukiyoyin su daga waɗannan ƴan ta’adda da suka hana gudanar da kiwo cikin kwanciytar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *