Babu hannuna a korar Wike daga PDP – Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar PDP ta ɗauka na korar ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu daga jam’iyyar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinta X, Ahmadu Fintiri ya ce ya yi imanin cewa babu abin da matakin zai haifar sai ƙara dagula jam’iyyar.
Da maraicen yau Asabar ne PDP ta fitar da sanarawar korar Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar saboda abin da ta kira yi mata zagin-ƙasa.
Jam’iyyar ta ce ta ɗauki matakin ne a wajen babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo, bisa amincewar mafiya rinjayen ƴaƴanta.
Sai dai gwamnan na Adamawa wanda ke cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ya nesanta kansa da matakin.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jam’iyyar ta rungumin hanyoyin sasanci domin warware duka matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta.
