Babu buƙatar jiran umarni a yaƙi da matsalolin tsaron Najeriya – Christopher Musa

Sabon ministan tsaron Najeriyar Janar Christopher Musa mai ritaya ya buƙaci ilahirin ma’aikatan da ke ƙarƙashinsa masu kaki da fararen hula da su yi amfani da dukkanin matakan da suka dace a yaƙin da ya faro da ayyukan ta’addanci ba tare da jiran umarni ba.
Yayin jawabinsa na farko bayan isa ofishi a shalkwatar tsaron Najeriyar da ke Abuja jiya Juma’a, Musa ya sake nanata alwashinsa na gaggauta ɗaukar matakan da suka kamata wajen murƙushe barazanar tsaron da ƙasar ke gani tare da gabatar da sabbin tsare-tsaren da za su samar da maslaha ga jama’ar ƙasa ta fuskar tsaro.
Janar Musa, wanda kafin yanzu shi ne babban hafson tsaron Najeriyar ya bayyana cewa da gasgatawar da shugaban ƙasar ya yi masa da kuma cikakken goyon bayan jama’a ne ya dawo shalkwatar a matsayin ma’aikaci, a don haka babban aikin da ke gabansa shi ne ɗaukar matakan gaggawa da suka kamata wajen magance matsalolin tsaron ƙasar.
