Babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh ya rasu

Allah Ya yi wa babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh rasuwa.
Za a yi jana’izar marigayin a masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke Riyadh bayan sallar La’asar, kamar yadda Sarkin Saudiyya ya sanar.
Haka kuma, za a yi masa Salatul Gaib a masallacin Ka’aba, masallacin Annabi Muhammad SAW, da dukkan masallatan da ke Saudiyya.
Sheikh Abdul Aziz ibn Abdullah Al-Sheikh, wanda ya kasance babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya, ya shahara wajen kyakkyawan shugabanci da tasiri a al’umma.
Ya kasance mutum mai girmamawa da kyawawan halaye, wanda mutane da dama suka ɗauka a matsayin jagora wajen shari’a da addini.
