Babban layin wutar lantarki ya sake lalacewa a Najeriya

0
1000442046
Spread the love

Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarkin ƙasar a ranar Talata,Wannan shi ne karo na biyu da babban layin wutar ke fuskantar irin wannan matsala a shekarar 2026 wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki a fannoni da dama na ƙasar.

Layin wutar ya fara lalacewa ne a ranar Juma’a da ta gabata.

Masana da hukumomi sun danganta lalacewar da tangarɗar na’ura da rashin cikakken gyare-gyare da kulawa ga manyan layukan wuta.

Bincike ya nuna cewa dukkanin tashoshin samar da wutar lantarki 23 da ke haɗe da babban layin sun daina aiki gaba ɗaya.

A halin yanzu, babu cikakken bayani kan abin da ya janyo wannan lalacewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *