‘Ba za mu zuba ido a ci gaba da kashe kiristoci a Najeriya ba’

Shugaba Trump na Amurka na nanata iƙirarin da ya yi cewa ”Kiristoci na fuskantar mummunan barazana a Najeriya”.
Yayin wani jawabi da ya gabatar a fadar gwamnatin ƙasar, Mista Trump ya ce Amurka ba za ta ci gaba da zura idanu ana kashe Kiristoci a Najeriya da sauran ƙasashe ba.
”Masu tsattsauran kishin Musulunci na ci gaba da kashe dubban Kiristoci a Najeriya, kan haka ne na sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake nuna damuwa a kansu”
”A shirye muke don kare ƴan’uwanmu Kiristoci a faɗin duniya”, in ji Trump.
Shugaban na Amurka ya ce a yanzu haka ya umarci Majalisar Wakilan Amurka ta gaggauta binciken wannan lamari tare da kawo masa rahoto cikin gaggawa.
