Ba za mu lamunci rashin da’a a reshen Adamawa ba – ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani aiki na rashin da’a da zai iya kawo cikas ga kokarin gina hadin kai da karfafa jam’iyyar a jihar Adamawa ba.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, jam’iyyar ta nuna damuwa kan karuwar rarrabuwar kawuna tsakanin mambobinta a jihar.
Jam’iyyar ta tunatar da membobin cewa a taron da ta gudanar a ranar 8 ga Oktoba, 2025, Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) ya amince da kafa Kwamitocin Zartarwa na Rikon kwarya don kula da harkokin jam’iyyar a jihohi daban-daban a yanzu.
Bayan abin da ta bayyana a matsayin bincike mai kyau, ADC ta tabbatar da cewa tsarin da aka gudanar a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, kuma Mataimakin Shugaba na Arewa maso Gabas ke kula da shi, ya yi daidai da amincewar NWC da jagororinta.
Wannan tsari, a cewar sanarwar, ya nada Barista Sadiq Dasin a matsayin Shugaban Rikon Kwarya na ADC a Jihar Adamawa.
Yayin da yake yaba wa shugabancin Dasin, ADC ta yi kira ga dukkan membobin da ke cikin shirye-shiryen da suka yi daidai da juna da su sake tunani su kuma bi hanyar sulhu.
