Ba na so na tsaya takara a 2027 – El-Rufai

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba ya tunanin tsayawa takara a zaɓen ƙasar na shekara ta 2027 ba.
Ya ce dawowarsa harkar siyasa kwanan nan ba don neman muƙami ba ne, sai don tallafa wa shugabanci nagari a dukkan matakai.
El-Rufai ya yi wannan bayani ne yayin wani taron siyasa a jihar Kaduna ranar Laraba.
Ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu, inda ya ce ta gaza.
Nasir El-Rufa’i na cikin manyan ƴan siyasar Najeriya da suka yanke shawarar kafa hadakar ƴan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar a zaɓen ƙasar na 2027.
Tsohon gwamnan na daga cikin wadanda suka mara wa APC baya a zaɓen 2023 da ya gabata, lokacin da shugaba Bola Tinubu ya yi nasara, sai dai ɗan siyasar ya raba gari da jam’iyyar watanni bayan hawan Tinubu kan mulki, inda ya koma jam’iyyar SDP.
Daga baya kuma ya bayyana cewa zai kasance cikin jam’iyyar ADC wadda a yanzu haka ƴan adawar ke amfani da ita a matsayin lemarsu.
