Ba ma goyon bayan kara albashi ga masu rike da mukaman siyasa — ADC

Sabuwar jam’iyyar hadakar ‘yan adawa a Najeriya ta ADC ta bayyana damuwa a game da shirin kara albashin masu rike da mukaman siyasa a kasar.
Jam’iyyar ta bayyana shirin da cewa ”yin biris ne”, kuma cin fuska ne ga al’ummar kasar da ke fama da katutun matsalolin rayuwa da suka hada da hauhawar farashin kaya da tashin farashin mai da kwauron albashi mafi kankanta da dai sauran matsaloli.
Daya daga cikin masu magana da yawun jam’iyyar hadakar ta ADC, Faisal Kabiru, ya shaida wa manema labarai cewa, duba da halin da talakan Najeriya ke ciki wanda abinci ke gagararsa ballantana magance wasu matsaloli na rayuwa, ace za a karawa mutanen da suke rayuwa yadda suke so saboda suna da hali albashi.
Ya ce,” Mu a matsayinmu na jam’iyya munyi alawadai da wannan mataki na karawa ‘yan siyasa albashi, domin suna samun alawus su yi duk abin da suke bukata, sannan gashi gwamnati na dauke musu yawancin bukatunsu a don haka ya za a hadashi da mutumin da ke daukar albashin naira dubu 70.”
