Australia ta amince da kafa ƙasar Falasɗinu a taron MDD

0
1000065380
Spread the love

Australia ta shiga cikin jeren ƙasashen duniya da ke shirin amincewa da kafuwar ƙasar Falasɗinu a babban taron MDD na watan Satumba.

Firaminista, Anthony Albanese ya ce sun yanke wannan shawarar la’akari da yanayi na bala’in bukatar jin-kai a Gaza da kuma mamayar da Isra’ila ke yi wanda ya saɓa ƙa’ida a gabar yamma da Kogin Jordan.

Ya ce zamu yi aiki da ƙasashen duniya wajen tabbatar da wannan ‘yanci, ganin yanayin da ake ciki a Gaza ya zarta fargabar da ƙasashen duniya suka nuna, sannan Isra’ila ta bijirewa dokokin duniya kan bada agaji.

Mista Albanese ya ce Hamas ba ta da makoma a ƙasar Falasdinu kuma bai dace fararan-hula su kasance masu biyan laifukan da wata ƙungiya ta aikata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *