Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, kuma jigo a jam’iyyar haɗaka ta ADC ya nuna damuwa kan ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a da aka samu a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja na ranar Asabar, yana mai zargin cewa hakan na nuna yadda ake yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa yawan jama’ar da suka fito zaɓen Abuja bai kai kashi 20 cikin 100 ba wata alama da ke nuna halin da dimokuraɗiyyar Najeriya ke ciki a yanzu.
Ya ce “Ƙarancin masu kaɗa kuri’a da aka samu a babban birnin ƙasar ba abin mamaki ba ne, illa sakamakon yanayin siyasa da ya ce ya cika da rashin haƙuri da tsoratarwa da kuma rage ƙarfin muryoyin adawa.
“A cewarsa, “idan ’yan ƙasa suka daina yarda cewa ƙuri’unsu na da tasiri, dimokuraɗiyya ya fara mutuwa.”
