Atiku ya ƙaryata labarin baiwa Yerima sabuwar mota kirar SUV

0
20250601_134212
Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, wani jami’in sojin ruwa da ya yi jayayya da Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Neysom Wike sabuwar mota kirar Toyota SUV.

Wani rahoto mai taken “Atiku Abubakar ya bai wa Yerima sabuwar mota kirar Prado SUV ta 2024” ya yadu a shafukan sada zumunta.

Amma Atiku, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Paul Ibe ya fitar, ya ce labarin an ƙirƙira shi ne gaba ɗaya, yana kira ga jama’a da su yi watsi da shi.

Sanarwar ta ce, “Mai girma Atiku Abubakar, bai bai wa Laftanar Ahmed Yerima ko wani mutum sabuwar mota kirar Toyota SUV ba, sabanin rahotannin karya da ke yawo a shafukan sada zumunta a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *