APC ta yiwa Atiku raddi kan tsokacin sa gameda harin Boko Haram a Adamawa

0
APC-Atiku
Spread the love

Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa ta mayar da martani ga kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan harin da ‘yan Boko Haram suka kai wa al’ummar Wagga Mongoro a karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na jiha, Hon. Mohammed Abdullahi, ya fitar a Yola, ya zargi Atiku da rashin kula da tsaro da jin dadin jama’a duk da cewa yana cikin fargaba da rashin tabbas sakamakon harin da aka kai.

Ya kuma kara da cewa Atiku yana son bata sunan jam’iyyar APC ko ta halin kaka, duk da cewa jam’iyyar na yin aiki mai kyau wajen kawo karshen matsalan tsaro a Najeriya.

A cewar sa a yanzu Najeriya na karkashin masu hazaka, masu kishin kasa, da jajircewa wajen tafiyar da al’amura a halin yanzu, suna goyon bayan jiga-jigan sojojin mu da jami’an tsaro.

APC ta kara da cewa lokacin da ‘yan Boko Haram suka mamaye al’ummar Adamawa, suka raba mutane da gidajen su da iyalansu, Atiku ya yi shiru sai yanzu da ake kokarin shawo kan matsalan tsaro karkashin jam’iyyar APC yake neman maido da hannun Agogo baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *