Anyi arangama tsakanin dakarun Sudan ta kudu da Uganda a kan iyaka.

0
1000039652
Spread the love


Sojoji daga Sudan ta Kudu da na Uganda sun yi musayar wuta a kusa da iyakarsu lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan akalla mutum shida.

Mai magana da yawun rundunar sojin Uganda ya ce sojojin Sudan ta Kudu sun tsallaka iyakar Uganda ta bangaren yankin West Nile sannan kuma sun ki barin wajen.

Ya ce an kashe daya daga cikin sojojin kasarsu. Jami’ai a Juba sun ce an yi musayar wutar ne a iyakar inda aka kashe musu sojoji biyar.

Kasashen biyu dai sun jima suna da kyakkyawar alaka a tsakaninsu. Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya taimakawa ‘yan tawayen Sudan ta Kudun wajen kwatar ‘yancinsu daga Sudan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *