Ana zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaɓen Kamaru a Garoua

Al’ummar yankin Garoua na ƙasar Kamaru na ci gaba da gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.
Paul Biya mai kimanin shekara 92 ne dai ya lashe zaɓen domin ci gaba da mulki bayan kusan shekara 42 yana mulkin ƙasar.
Abokin takararsa Issa Bakary dai ya dage kai da fata cewa shi ne ya lashe zaɓen.
