Ana samun galaba kan ‘yan Boko Haram da ‘yan bindigan daji – Ribadu.

0
NSA_Nuhu-Ribadu-e1740495634848
Spread the love

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce an samu raguwar hare-haren Boko Haram da na ƴanbindiga har ma da rikice-rikice tsakanin al’ummomi a yankin arewacin ƙasar cikin shekaru biyu da suka wuce karkashin gwamnatin shugaba Tinubu – idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata.

Ya bayar da misalin cewa an kashe mutum 1,192 sannan an sace sama da 3,348 a jihar Kaduna a gwamnatin da ta shuɗe, yayin da sama da mutane 5,000 suka rasa rayukansu a jihar Benue a wannan lokaci.

Ribadu ya bayyana haka ne a yau Talata yayin jawabi a taron masu ruwa da tsaki na arewacin Najeriya wanda aka gudanar a jihar Kaduna.

Ya ce nasarar da aka samu a yaƙi da rashin tsaro ya samo asali ne sakamakon umarnin da shugaba Tinubu ya bai wa jami’an tsaro kan bin tsarin tabbatar da tsaro na bai-ɗaya.

Ya ƙara da cewa an samu nasarar sakin mutum 11,259 waɗanda aka yi garkuwa da su a watan Mayu kaɗai – a wasu samame daban-daban da sojojin Najeriya suka kai a arewa maso yamma.

Ribadu ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun kashe shugabannin ƴanbindiga da mambobinsu da dama a jihohin Zamfara da Kaduna da kuma Katsina.

Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna Uba Sani kan amfani da hanyoyi daban-daban wajen shawo kan matsalar tsaro a kudancin jihar da Birnin Gwari har ma da wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *