Ana ce-ce-ku-ce kan zargin ƙirƙirar hoton Tinubu da fasahar AI

0
1000432202
Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa fadar shugban ƙasa ta wallafa wani hoton shugaba Bola Tinubu da takwaran aikinsa na Rwanda Paul Kagame, wanda aka haɗa da ƙirƙirarriyar basira, wato AI.

Babban abin da ya janyo ce-ce-ku-cen a shafukan sada zumunta shi ne yadda aka ga tambarin fasahar AI na kamfanin Twitter, wato Grok a jikin hoton da aka wallafa na Tinubu a jiya Lahadi.

Wani mai taimaka wa Najeriya kan yaɗa labarai, Temitope Ajayi ya ce ba haɗa hoton aka yi da ƙirkirarriyar basira ba, sai dai an yi amfani da fasahar ce wajen “inganta kyawun hoton.

“Ya bayyana cewa an ɗauki hoton ne da wayar hannu, kuma sai hoton ya kasance bai da inganci, wanda hakan ya sa aka yi ƙoƙarin inganta shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *