Ana ƙaddamar da rundunar tsaro da kare unguwanni ta jihar Kano

Yanzu haka gwamnatin jihar Kano na ƙaddamar da rundunar tsaro da kare unguwanni na mutum 2000 a filin wasa na Sani Abacha, a wani mataki da ake sa ran zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da rage laifuka a sassan jihar.
An kafa rundunar ne domin taimakawa hukumomin tsaro na ƙasa wajen sa ido da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a matakin unguwanni.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar za ta ƙunshi matasa da aka horas musamman kan ayyukan tsaro da tattara bayanan sirri da kuma aiki tare da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Gwamnatin jihar ta ce za a rarraba rundunar a ƙananan hukumomi daban-daban domin tabbatar da tsaro a kasuwanni da makarantun da unguwanni da sauran muhimman wurare.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta jaddada cewa ƙaddamar da rundunar na daga cikin ƙoƙarin da take yi na samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma bai wa al’umma kwarin gwiwar rayuwa cikin aminci.
Ta yi kira ga mazauna jihar da su ba da haɗin kai tare da tallafa wa rundunar domin ta samu nasara a aikinta na kare lafiyar jama’a.
