An zargi RSF da kashe tare da cin zarafin naƙasassu yayin ƙwace El Fasher a Sudan
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi dakarun ƙungiyar RSF da kai wa mutane masu lalurar nakasa hari tare da cin zarafinsu da kuma kashesu a lokacin da suka ƙwace birnin El fasher a yankin Darfur a watan octoban daya gabata.
A cikin wani sabon rahoto da ta fitar, ƙungiyar ta ce mayaƙan RSF sun riƙa neman mutane masu nakasa da kuma tabin hankali.
Ƙungiyar human rights watch ta yi magana da mutum 22 da suka tsira da kuma shaidu inda ta tattara bayanai akan waɗanda aka kashe da waɗanda aka yi wa duka ko aka tsare ba tare da sun aikata wani laifi ba.
Waɗanda suka tsira sun faɗawa ƙungiyar cewa da dama daga cikin waɗanda suka rasa gaɓɓoɓinsu mayakan RSf sun daukesu a matsayin sojojin Sudan kuma an kashesu.
Kawo yanzu kungiyar RSF ba ta ce komai kan zargin
