An tsawaita wa’adin aikewa da bukatar aikin Hukumomin shige da fice, Civil Defence, da sauran su.

0
1000051781
Spread the love

Hukumar Tsaro ta Civil Defence, da Hukumar kula da Gyaran hali, da Hukumar kula da kashe Gobara da Hukumar Kula da Shige da Fice, CDCFIB, ta sanar da tsawaita wa’adin aika bukatar neman aikin daukar ma’aikata na 2025 da ke gudana.

A wata sanarwa da sakataren hukumar Manjo Janar (Rtd) A.M Jibril, ya fitar a ranar Lahadi. Hukumar ta ce tashar daukar ma’aikata, wadda aka shirya rufe a ranar Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025, za ta ci gaba da zama a bude har zuwa ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025.

A cewar sanarwar, “Wannan matakin an tsara shi ne don samar da ƙarin dama ga masu neman izinin shiga cikin kowan daukar ma’aikata kwanan nan.

Hukumar ta shawarci irin wadannan masu nema da su tantance bayanansu tare da kammala aikin, tare da lura da cewa “da zarar an kammala nasara, za a samar da takardar shaidar da aka samar a baya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *