An shiga ruɗani a Katsina yayin da sojoji suka kashe mahaifin shugaban ‘yan fashi a Malumfashi

Ana ci gaba da zaman dar-dar a yankin karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina bayan kisan Alhaji Ibrahim Nagode, mahaifin wani shugaban ‘yan fashi da makami da ake nema ruwa a jallo, a lokacin wani farmaki da jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian suka kai.
Nagode, mai shekaru 60, yana zaune ne a kauyen Na’alma kuma shine mahaifin Haruna Ibrahim, wanda aka fi sani da Fada.
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa harbin ya faru ne yayin da Fada ke komawa ƙauyen bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma kwanan nan tsakanin ‘yan fashi da makami da al’ummomi a yankin.
Jami’an tsaro sun lura cewa yankin ya kasance cikin rudani bayan da bayanai suka nuna cewa ‘yan fashi da makami suna sake taruwa a kusa.
An tura sojoji na hadin gwiwa don hana hare-hare a yankin, amma aikin nasu ya kai ga harbin Nagode da ya yi sanadiyyar mutuwar sa.
Hukumomin tsaro na jihar sun kama dukkan ma’aikatan CJTF da ke da hannu a lamarin.
Hukumomin suna sa ido sosai kan lamarin, tare da fargabar cewa kisan na iya haifar da ramuwar gayya da kuma kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya a yankin.
Majiyoyi sun jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa da kuma girmama yarjejeniyar zaman lafiya da ake da ita don gujewa ci gaba da tashin hankali.
Jami’an tsaro sun bukaci mazauna yankin da su kasance cikin shiri su kuma bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi a cikin al’ummominsu.
