An sanya ranar zaɓe a Uganda inda Shugaba Museveni zai nemi tsawaita mulkinsa

Hukumar zaɓen Uganda ta sanya ranar 15 ga watan Janairun shekara mai zuwa a matsayin lokacin da za a gudanar da zaɓen ƙasar, inda Shugaba Yoweri Museveni zai nemi tsawaita mulkinsa zuwa kusan rabin ƙarni.
Museveni, wanda ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar tun 1986, shi ne shugaba na huɗu mafi daɗewa akan karagar mulki a Nahiyar Afrika, ya sauya kudin tsarin mulkin ƙasar har karo biyu, inda aka cire taƙaita wa’adin mulki da kuma shekaru, domin ya samu damar ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban ƙasar.
A cewar, babban ɗan adawa a zaɓen da ya gabata Robert Kyagulanyi, ya ce Museveni ya lashe zaɓen ne sakamakon yin aringizon ƙuri’u da tsoratar da masu jefa ƙuri’a da sauran dabarun maguɗin zaɓe.
Sai dai tuni tun a wancan lokaci manyan jami’an jam’iyya mai mulkin ƙasar, suka yi watsi da wannan zargi, tare kuma da nanata cewa Museveni ya lashe zaɓensa ne ta halastacciyar hanya.
Yanzu haka dai, ƴan takara 6 ne da ke wakiltar ƙananan jam’iyyu za su fafata a takarar shugabancin ƙasa a zaɓen mai zuwa, yayin masu jefa ƙuri’a za su zaɓi ƴan majalisar dokokin ƙasar.
Dama dai, masu suka, sun sha yin Allah wadai da yadda gwamnatin Museveni ke murƙushe abokan hamayya, tare da zarginta da take haƙƙin bil’adama, baya ga cin hanci da rashawa da ya yi wa gwamnatin katutu.
