An sake samun ɓullar Cutar Ebola a Jimhoriyar Dimokaraɗiyyar Congo

Aƙalla mutum 15 ne suka mutu sakamakon sake ɓullar cutar Ibola, a Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo.
A wannan juma’a ne hukumomin lafiyar ƙasar suka ayyana sake ɓullar cutar ta Ebola a lardin Kasai, da ke tsakiyar Congo inda aka sanar da mutuwar wannan adadi, wanda ya haɗa da wanda aka samu tun daga ƙarshen watan Agusta.
Bayanan hukumar lafiya ta ƙasar, na nuni cewa ƙwayar cutar a karo na farko ta bullu ne a ranar 20 ga watan da ya gabata na Agusta.
Ebola kwayar cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar saduwa da ruwan jiki kamar jini, amai, ko maniyyi.
Cututtukan da take haifarwa ba su da yawa, amma suna da tsanani, kuma a lokuta da yawa, suna saurin kisa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), tace a halin yanzu ta samarwa Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo, allurai dubu biyu (2,000) kuma tuni sun isa Kinshasa, daga yanzu zuwa ko wanne lokaci za ƙarasa da su yankin na Kasai.
