An kashe ƴansanda uku tare da jikkata biyu a Katsina

Aƙalla ƴansanda uku ne aka kashe sannan biyu suka jikkata a wani harin kwantan-ɓauna da ƴanbindiga suka kai jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne ranar Talata, 27 ga watan Janairu, lokacin da ƴansanda ke aikin sintirin da suka suba yi a ƙauyen Guga da ke karamar hukumar Bakori na jihar ta Katsina.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an kai harin da lokacin da jami’an ƴansanda suka je yankin domin daƙile wani hari da ɓata-gari suka yi niyyar kai wa, inda daga nan suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
Kakakin ƴansandan jihar DSP Abubakar sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.
Ya ƙara da cewa an fara gudanar da bincike domin kama waɗanda suka kai harin, don hukunta su.
