An kashe wani mutum a rikicin ƙabilanci a Yobe

Mutum ɗaya ya mutu wasu biyu kuma sun sami munanan raunuka bayan wani mummunan rikici tsakanin ƙungiyoyin matasa biyu a yankin karamar hukumar Tarmuwa, in ji rundunar ‘yan sandan jihar Yobe.
A cewar majiyoyi, lamarin ya faru ne a ranar 12 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 10:22 na safe, lokacin da Manu Ahmadu, mai shekaru 20, da Ali Isah, mai shekaru 22, daga ƙauyen Koromari, a yayin da suke kiwon dabbobinsu a cikin daji na ƙauyen Kurmari.
Mas’udu Rabiu, mai shekaru 20, da Abdullahi Abubakar, mai shekaru 23, daga wannan yanki ne suka kai musu hari, dauke da baka, kibiya, da sanduna, bayan wani rikici da ya faru a baya.
An zargi Abdullahi Abubakar da harbin Manu Ahmadu a ƙirji da kibiya sannan ya bugi Ali Isah a kai da ciki a lokacin rikicin, Abdullahi Abubakar ya ji rauni sakamakon kibiya a ciki, yayin da Mas’udu Rabiu ya samu raunuka a hannuwa biyu.
An garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa Babban Asibitin Dapchi domin yi musu magani, inda ma’aikatan lafiya suka tabbatar da mutuwar Manu Ahmadu.
An kama wadanda ake zargi guda biyu kuma a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda.
