An kashe sojoji 80 a harin ƴanbindiga a Burkina Faso

0
1000438262
Spread the love

Rahotanni daga Burkina Faso na cewa gomman sojojin ƙasar ne suka rasa rayukkansu bayan da mayaƙan Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al-Qaeda suka mamaye sansaninsu da ke garin Titao a arewacin ƙasar a ranar Asabar din da ta gaba ta.

Kawo yanzu dai babu wani bayani daga sojoji ko gwamnati.

Amma wata kafar yaɗa labarai mai alaƙa da ‘yan adawa mai suna Sahel Alerte, wadda ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna yadda mayaƙan ke daukar hoton gawarwakin, ta ce akalla sojoji da ‘yan sa-kai masu goyon bayan gwamnati 80 ne suka mutu a harin

Ita ma gwamnatin Ghana ta tabbatar da mutuwar ‘yan kasar bakwai a Lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *