An kara kudin neman fasfo na Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta sanar da sake karin kudaden fasfo din Najeriya.
Gwamnati ta sanar da cewa karin zai fara aiki ne daga Satumba 1, 2025.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin hukumar shige da fice ta Najeriya, A.S Akinlabi ya fitar ranar Alhamis.
Akinlabi ya bayyana cewa karin kudin na da nufin tabbatar da inganci da ingancin fasfo din Najeriya wanda zai fara aiki a ranar 1 ga Satumba, 2025.
A cewar sa karin kawai ya shafi kudaden neman fasfo ne da ake yi a Najeriya, wanda a yanzu sabbin hanyoyin biyan fasfo mai shafuka 32 mai aiki na shekaru 5 zai koma akan N100,000 da fasfo mai shafuka 64 tare da aiki na shekaru 10 akan N200,000.
