An daƙile yunƙurin jiyun mulki a Burkina Faso

Hukumomin Burkina Faso sun bayyana cewa sun gano tare da kuma daƙile wani shirin juyin mulki da aka tsara don kashe shugaban sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré, da kawo rashin kwanciyar hankali a kasar a karshen mako da ya gabata.
Ministan tsaro ƙasar, Mahamadou Sana, ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya yi a daren ranar Talata, inda ya nuna wani bidiyo da ke nuna yadda aka shirya kai hari ga shugaban kasar ko dai ta hanyar harbin shi kai tsaye ko kuma ta hanyar sanya bam a gidansa a daren 3 ga watan Janairu, kafin a kai farmaki ga sauran manyan jami’an soja da na farar hula.
Ministan ya kuma zargi tsohon shugaban kasar da aka hamɓarar a shekarar 2022, Laftanar Kanar Henri Damiba, da tsara juyin mulkin.
Rahotanni sun ce tsohon shugaban ya tara sojoji da magoya bayansa fararen hula inda ya samu kudade kimanin CFA miliyan 70 daga Côte d’Ivoire sannan ya tsara lalata sansanin harba jirage marasa matuƙa kafin sojojin ƙasashen waje su shiga tsakani.
Ministan ya ce an kama mutane da dama kuma ana ci gaba da bincike, inda za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Tun bayan karɓar mulki a 2022, Traoré ya fuskanci yunƙuri da dama na juyin mulki da tashin hankali daga kungiyoyi masu iƙirarin jihadi.
