An bukaci iyayen yara dasu bada hadin kai wajen kai yaran su Alluran Riga kafi

Mai Jimillan Gundumar Bole, Malam Abdulmumini Abubakar, ya bukaci iyaye a Bole, dake Yolde Pate da su fifita allurar rigakafi ga ‘ya’yansu.
Da yake jawabi a wani dandalin taro da Ƙungiyar Fathers for Good Health ta shirya a karkashin Kwamitin Ci Gaban Unguwa na Kwamitin Kula da Lafiya a matakin farko na Shagari, Yola, Mai Jimillan na Bole ya jaddada cewa wadannan shirye-shiryen kiwon lafiya suna da matukar muhimmanci, musamman bayan ambaliyar ruwa da kalubalen al’umma kwanan nan.
Ya nuna farin cikin sa da wannan ƙungiya, wanda ta yi bitar aikin allurar rigakafi da aka kammala kwanan nan, yana nuna karfin hadin gwiwa tsakanin al’umma.
Mallam Abdulmumini Abubakar ya yaba wa gwamnati kan tsarin da ta bi wajen aiwatar da shi da kuma masu ruwa da tsaki kan jajircewarsu a lokacin aikin.
Shugaban Fathers for Good Health, na karamar hukumar Yola ta Kudu, Alhaji Abubakar Ahmed ya yaba wa ƙungiyar Bole Yolde Pate kan shirinsu na gudanar da aikin riga kafin, wanda ya kafa misali ga ayyukan kiwon lafiya a nan gaba a cikin al’umma.
Shehu Usman Aliyu, wanda ya wakilci kungiyar a yankin Bole Yolde Pate, ya yi kira da a haɗa ƙungiyar cikin tsarin ayyukan kiwon lafiya, yana mai jaddada cewa wannan zai haifar da ingantaccen aikin kiwon lafiya.
Mrs. Balthiya Vincent da Alhaji Abdullahi Ishaq, waɗanda suka halarci aikin, sun nuna muhimmiyar rawar da kungiya ke takawa wajen ƙara yawan waɗanda za su amfana.
Sun lura cewa alluran rigakafi suna da mahimmanci ga makoma mai kyau ta hanyar yin aiki tare da rungumar waɗannan shirye-shiryen, don gina al’umma mai ƙarfi da juriya.
A cikin jawabinsa, Mai Kula da Yankin na Aikin Allurar Rigakafi, Kwamared Umaru Ahmed, ya gode wa masu ruwa da tsaki kan haɗin gwiwarsu, yayin da Mista Yohanna Manje ya shawarci masu ruwa da tsaki da su yi amfani da tausayi, sulhu, jajircewa da haɗin gwiwa wajen magance rikice-rikice yayin gudanar da ayyukansu.
