Adamawa: Sabon kwamishinan ƴan sanda ya kama aiki
Sabon kwamishinan ƴan sanda na Adamawa
Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Adamawa, CP Kabir Umar Hassan, ya kama aiki a ranar 27 ga Maris, 2026 a matsayin kwamishina na 33 na rundunar ƴan sanda a jihar.
CP Hassan gogaggen jami’i ne da ya shafe shekaru yana aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da bincike, gudanarwa da ayyukan tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.
Kafin wannan muƙami, ya kasance Kwamishinan ‘Yan Sanda a hedikwatar rundunar da ke Legas.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta buƙaci jama’a da su ci gaba da ba da haɗin kai da sahihan bayanai domin inganta tsaro a jihar.
