Adamawa ce ke kan gaba yayin da mutum 616,873 ke neman aikin ‘yan sanda
Hukumar kula da ‘Yan sanda ta ce Jihar Adamawa ce ta fi yawan masu neman aikin a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya, yayin da aka samu mutum 616,873 a duk fadin kasar.
Daga cikin jimillar masu neman aikin, Hukumar PSC ta ce 434,604 sun cancanci a ci gaba da tantance su, yayin da 121,596 ba su cancanta ba kuma 60,673 ba su da inganci.
Hukumar ta ce 442,592 daga cikin masu neman aikin maza ne, yayin da 114,640 mata ne.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Shugaban kwamitin kula da harkokin ‘Yan sanda na PSC, DIG Taiwo Lakanu (mai ritaya), ya ce Adamawa ta sami 38,989 masu neman aikin, sai Benue da 34,511; Kaduna, 30,397; da Borno, 24,009.
Ya ƙara da cewa za a tura waɗanda suka yi nasara zuwa kwalejojin ‘yan sanda da aka keɓe don horo kafin a tura su zuwa kwamitoci da sansanonin aiki don gudanar da aiki.
