‘Adadin ɗalibai da malaman da aka sace a makarantar Neja ya kai 315’

0
1000315704
Spread the love

Adadin ɗalibai da malaman makarantar sakandiren cocin St. Mary da ƴanbindiga suka sace a ranar Alhamis da daddare ya kai 315 kamar yadda ƙungiyar Kiristocin ƙaar CAN ta bayyana.

Gidan Talbijin na Channels a Najeriya ya ambato, shugaban ƙungiyar CAN reshen jihar Neja, Most. Rev. Bulus Dauwa Yohanna na bayyana haka bayan kammala aikin tantance ɗaliban makarantar.

Yohanna ya ce, “Bayan mun kammala aikin tantance ɗaliban ta hanyar tuntuɓar iyayensu ga waɗanda muke zaton sun gudu sun koma gida, sai muka gano cewa akwai ƙarin ɗalibai 88 da muke kyautata zaton suna hannun maharan”.

“Akwai iyaye da dama da muka yi zaton cewa ƴaƴansu sun koma gida a lokacin da aka tsarwatsa makarantar, amma sai aka shaida mana cewa iyayen sun zo makarantar domin neman ƴaƴansu”, in ji shi.

Yohanna ya ce kawo yanzu akwai ɗalibai 303 da malamansu 12 da ba a gani ba tun bayan harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *