Abba na kan turbar komawa wa’adi na biyu – Ganduje

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnan Kano “Abba Kabir Yusuf na kan turbar komawa wa’adi na biyu” a zaɓen shekarar 2027.
Ganduje ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, inda ya yaba da matakin gwamnan na sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Ganduje ya ce shigowar gwamna Abba cikin APC zai ƙara ƙarfafa jam’iyyar a jihar Kano da ma Arewa gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa haɗin kan manyan jagororin jam’iyyar zai taimaka wajen tabbatar da nasara a zaɓuka masu zuwa.
A jiya Litinin ne dai Gwamna Yusuf ya kammala komawa jam’iyyar APC a hukumance, bayan watanni na raɗe-raɗin siyasa da hasashe kan makomarsa.
An gudanar da taron sauya sear gwamnan a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka shirya a gidan gwamnatin jihar Kano, wanda ya ja hankalin manyan ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyar.
Mahalarta taron sun bayyana komawar gwamnan a matsayin babban sauyi da zai sake fasalta siyasar Kano gabanin zaɓen 2027.
