A daina yaɗa jita-jitar sauya Kashim Shettima – APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar za ta sauya Mataimakin Shugaban Ƙasar, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekara ta 2027.
Jam’iyyar ta ce rahotannin ba su da tushe, “kuma tsantsar jita-jita ce da ke da nufin haddasa ruɗani da rikici a harkokin siyasar ƙasar”.
APC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Felix Morka, ya fitar.
A Najeriya an daɗe ana raɗe-raɗin cewa jam’iyyar za ta iya sauya mataimakin shugaban ƙasar gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.
Tun farko haɗin Bola Tinubu da Kashim Shettima ya sha suka daga wasu ɓangarorin ƙasar kasancewar ana ganin hakan ya saɓa da al’adar da aka saba da ita ta saɓawar addinin shugaban ƙasa da mataimakinsa.
Sai dai a lokuta da dama masu alaƙa da jam’iyyar mai mulki sun ce an yi hadin ne a matsayin wata dabara ta siysa da neman cin zaɓe a shekara ta 2023.
Ana sa ran harkokin siyasa za su rincaɓe a cikin wannan shekara ta 2026 a Najeriya, gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara mai zuwa, inda ake sa ran Tinubu zai sake yin takara domin neman wa’adin shugabanci na biyu na tsawon shekara huɗu.
