A daina siyasantar da rashin tsaro’ – Uba Sani yayi kira ga ƴan adawa

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya shawarci ‘yan adawa da su daina siyasantar da matsalar rashin tsaro a Najeriya, Gwamnan ya bayar da wannan nasihar ne a wajen gabatar da Littafin da Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya rubuta, wanda Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara zuwa harshen Larabci.
Gwamna Uba Sani ya wakilci shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin babban bako na musamman, sannan kuma shi ne babban bako a wajen taron wanda kungiyar Jama’atu Izalatul Bidáh Wa ‘iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta shirya a ranar Asabar.
Ya kara da cewa, rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma ya bambanta da ta’addancin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, wanda akida ce ke haddasawa, yayin da a yankin Arewa maso Yamma kuwa talauci, rashin aikin yi da rashin kula da al’ummar karkara ne ke kan gaba wajen matsalan‘yan fashi.
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamnan ya nuna cewa “ba za a iya magance rashin tsaro ta hanyar amfani da bindigogi kawai ba.
