A ƙalla mutum 35 ne suka mutu sakamakon fashewar tankar mai a Neja

0
1000239253
Spread the love

Ana fargabar mutuwar mutane da dama a haɗarin wata tankar mai data kama da wuta a babbar hanyar Agaie zuwa Bida da ke cikin ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja da tsakar ranar yau Talata.

Bayanai sun ce wannan haɗarin ya haddasa cunkoson ababen hawa a mashin na Agaie zuwa Bida wanda tuni hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta tabbatar da faruwar lamarin kodayake bata fayyace adadin mutanen da suka mutu a ibtila’in ba.

Shugabar hukumar ta FRSC a jihar Neja Hajiya Aishatu Sa’adu ta ce afkuwar haɗarin da kuma rashin kyawun hanya ya haddasa dagulewar lamurra sakamakon cunkoson ababen hawa a wannan yammaci.

Haka zalika hukumar ta ce lalacewar titunan da za su sada jama’a da yankin da aka samu faruwar haɗarin, ya sanya jinkirin isar tawagar jami’an agaji don kai ɗauki ga waɗanda wannan ibtila’i ya rutsa da su.

Alƙaluman da Daily Trust ta tattara sun ce mutane da dama sun mutu akwai kuma wasu fiye da 40 da suka jikkata, bayan faɗuwar tankar tun da tsakar rana a kan titin na Essam mai tazarar kilomita 4 daga garin Badeggi.

Bayanai sun ce Tankar ta ɗauki tsawon sa’o’i bayan faɗuwa gabanin fashewa, kuma mutane sun yi amfani da damar faɗuwarta wajen kwasar man da ya zube.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *